Saturday, January 26, 2019

NASIHA AKAN ZABAN 2019



 *Nasiha Kan Zaɓen Bana (2019) #(2)*

Godiya ta tabbata ga Allaah Ubangijin Halittu. Tsira da Amincin Allaah su tabbata ga Shugaban Manzanni, shi da Alayensa da Sahabbansa da sauran Salihai.

Wani ne yake ganin wai bai kamata malamai su riƙa tsoma tsarkakan bakunansu a cikin al’amuran siyasar dimokuraɗiyyar ƙasar nan ba, musamman ma abin da ya shafi zaɓe. Watau: Wai bai dace a matsayinsu na manyan malamai da ake girmamawa su riƙa kiran jama’a ga cewa: Ku zaɓi wane ne, ban da wane ba!

Shi ne ni kuma a matsayina na almajirin malaman na ce: A ganina bai dace a ce malaman kar su yi hakan ba, saboda dalilai masu yawa:

[1] Babu inda makaho ko mai ido ɗaya zai yi daidai balle ma har ya fi mai ido biyu. Manyan Malamai gogaggun masana su ke da idanu masu kaifin gani a cikin al’amuran duniyarmu da rayuwarmu, kamar yadda suke da cikakken gani mai zurfi a cikin al’amuran addininmu da lahirarmu.

[2] Malamai irin waɗannan su ne suka san cikakken tarihin al’ummomin da suka shuɗe, kuma su ke da labarin al’ummomin da za su zo a nan gaba har zuwa Tashin Ƙiyama. Don haka su suka fi cancantar su yi mana saiti, kuma su nuna mana daidai a cikin rayuwa.

[3] Sannan kuma waɗannan malaman su ke da ilimi a kan dokokin Ubangiji na a-yi ko a-bari, kuma su ke da sani game da laifuffuka ko abubuwan da aikata su ke zama saɓo ne ga Ubangijinmu Tabaaraka Wa Ta’aala. Don haka rashin maganarsu a cikin al’amura ko kuma ƙin bin maganarsu ita ce cikakkiyar ɓatar da babu ɓacewa irinta.

[4] Haka kuma malamai su ne ke da cikakken sani a kan matsayin hukuncin kowane aiki: Wajibi ne ko mustahabbi ne a gefe ɗaya, sannan ko kuwa haram ne ko makaruhi ne a ɗaya gefen, ko kuwa dai halal ne kawai. Don haka su ke iya yin bayanin hanyar gaskiya a cikin dukkan rikici.

[5] Sannan kuma malamai su ne ke iya yi mana cikakkun bayanai a duk lokacin da al’amura suka rikice mana, muka rasa gaba muka rasa baya: Sai su nuna mana wace hanya ce ta dace mu bi don fita daga dukkan rikicin da ya same mu, da kaucewa afkawa cikin hallaka?

[6] Haka kuma a lokacin da abubuwa suka zama mana biyu, ko a inda muka ruɗe muka rasa yadda za mu iya fita daga kowace irin matsala su malamai ne dai ke iya fayyace mana har mu gane cewa: Wacce ce mafitar da ta yi daidai ko kuma ta yi kusa da daidai a shari’a?

[7] Hatta a kan wannan matsalar ta zaɓen siyasar bana (2019) wanda wasu ke tattaunawa, kuma suke kai wa da komowa a kanta: Malaman kirki na-Allaah ne ke iya kwantar da hankulanmu, su bayyana mana wanne ne daga cikin ’yan takara ya dace mu zaɓa.

[8] Malamai ne suke iya tuna mana abubuwan da muka manta na matsaloli da masifu da bala’o’in da muka shiga a wannan yankin na Arewacin Nijeriya a zamanin mulkin pdp kafin daga baya Allaah ya tausaya mana ya amshi addu’o’inmu, ya kawo mana wannan gwamnatin na apc mai ci a yau.

[9] Malamai ne suke iya tuna mana irin mutanen da aka hallaka a zamanin mulkin pdp a ƙauyuka da garuruwan Borno da Yobe da Adamawa da sauran wurare. Haka kuma da yawan mata da yara da tsofaffin da aka tarwatsa su daga gidajensu. Da kuma yadda aka riƙa bin su suna gudu cikin dazuzzuka, ana ta karkashewa, ban da matan da aka sace su aka tafi da su ba a san inda su ke ba!

[10] Malamai ne suke iya tuna mana yadda aka riƙa hallaka sojojinmu da gangar ta hanyar ɗiban su a kai fagen fama ba tare da an ba su cikakkun kuma ingantattun makamai ba. Sannan kuma idan sun gudu don tsira da rayukansu a kamo su a yanke musu hukuncin kisa domin wai sun ci amanar ƙasa! Duk a zamanin mulkin pdp!!

[11] Malamai ne ke iya bayyana mana hikimar da ta sa ’yan adawa suka zaɓo ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta pdp daga Arewacin ƙasar nan, kuma ya zama daga cikin ƙabila da addinin abokin takararsa na jam’iyyar apc. Domin a raba ƙuri’unmu ’yan Arewa ne, sannan ko a samu cin nasara a kanmu a lokacin zaɓen.

[12] Sannan kuma malamai ne dai suke iya bayyana mana cewa da gangar ’yan adawa suka zaɓo mai laifi a cikin tarihinsa suka tsayar da shi a matsayin ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa. Domin ko ba komai a iya samun dama da ikon sarrafa shi da jujjuya shi ta duk inda aka so, idan ya samu hayewa.

[13] Malamai su ne suke iya tuna mana zalunci da laifuffukan da jam’iyyar adawa ta tafka mana a baya, kafin Allaah ya kawo mana wannan gwamnatin mai ci. Ta yadda suka ƙyale ƙungiyar Boko Haram ta yi ta hallaka jama’armu ba tare da ɗaukar ƙwararan matakan dakatar da ita ba.

[14] Malamai ne ke iya tuna mana yadda gwamnatin baya ta siyasantar da al’amarin yaƙi da ƙungiyar ’yan ta’addan Boko Haram, watau ta mayar da rayukanmu ba a bakin komai ba. Har sai da Allaah Mabuwayi Mai Iko ya ƙwace mu daga hannunsu, ya bayar da mulki ga gwamnati mai ci!

[15] Malamai ne ke iya bayyana mana cewa a zamanin mulkin jam’iyyar nan ta ’yan adawa (pdp) ne fa aka yi mana mummunar ɓarnar da ba za mu iya mayar da irinta ba: Yadda aka kashe mana manyan malaman Sunnah a ƙasar nan, kuma har zuwa ƙarshen mulkinsu ba su kama kowa sun hukunta shi saboda hakan ba.

[16] Malamai ne ke iya fayyace mana cewa: A lokacin gwamnatin adawa ta pdp ne aka shiga masallaci da Asubah aka harbe babban malamin Sunnah Shaikh Ja’afar Mahmud Adam (Rahimahul Laah) ana gab da fara zaɓen 2007.

[17] Malamai ne za su iya tuna mana cewa: Tun daga wancan ranar baƙin-ciki da ta same mu sai da wannan jam’iyya da ta zama ta ’yan hamayya a yau, ta shafe shekaru takwas (2007-2015) tana mulki a kanmu, amma ba ta iya kamowa balle ta hukunta masu wancan ta’addancin ba!

[18] Malamai ne za su faɗa mana cewa: Wannan ɗan takaran da a yau ’yan jam’iyyar adawa suke son mu zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, shi ne mataimakin shugaban ƙasa a lokacin da aka yi mana wancan ta’addancin a birnin Kano!

[19] Malamai su za su tuna mana yadda aka riƙa bin manyanmu na Arewa ana ƙoƙarin hallaka su a lokacin mulkin jam’iyyar pdp, inda aka kai wa babban malamin ɗariƙar Tijjaniya Shaikh Ɗahiru Bauchi harin bam bayan ya tashi daga taron rufe tafsiri a Dandalin Murtala a Kaduna, abin da ya janyo mutuwar wasu mabiya, wasu da dama kuma suka jikkata!

[20] Har wa yau dai malamai su ne suke iya tuna mana yadda a zamanin mulkin pdp aka kai harin bam a Masallacin Jumma’a na ƙofar gidan Sarkin Kano, aka hallaka masallata masu ɗimbin yawa da suka je sallar Juma’a. Kuma har suka gama mulki ba mu ji mutanen da suka hukunta a kan hakan ba!

[21] Malamai ne dai suke iya tuna mana cewa: A lokacin mulkin wannan jam’iyyar adawa ta pdp ce aka zargi babban malamin Salafiyyah Albaaniy a Zariya da cewa shi ɗan Boko Haram ne, don haka aka ɗaure shi har sama da kwanaki arba’in! Kuma bayan kotu ta wanke shi daga zargin sai kuma aka bi duhun dare aka bindige shi har lahira bayan ya fito karatun Sahih Al-Bukhaariy a Tudun Wada Zariya, a 2014.

[22] Malamai ne za su iya gaya mana cewa: Idan ana tsama da Marigayi Malam Albaniy Zariya (Rahimahul Laah) don haka aka kashe shi, to meye kuma laifin matarsa da ɗansa da su ma aka kashe su a tare da shi? Yanzu ko domin wannan bai kamata a ce jam’iyyar pdp a lokacin ta matsa har sai ta tabbatar an kamo masu wannan laifin an hukunta su ba?!

[23] Malaman nan dai su ne suke iya tuna mana cewa: Tun daga wancan ranar da aka yi mana wancan aika-aika jam’iyyar nan ta pdp mai neman mu zaɓe ta a yau ba ta yi wani abin a-zo-a-gani ba wurin nema da hukunta makisan malamin shi da iyalinsa!

[24] Malamai su ne suke iya bayyana mana cewa: Kisan Shaikh Albaaniy (Rahimahul Laah) ya fi kama da na siyasa, saboda abin da aka san malamin ya yi na tsayin-daka wurin ganin an samu haɗin-kai a tsakanin musulmin ƙasar nan kafin zuwan zaɓen 2015, ga kuma yadda ya nace da a zaɓi jam’iyyar Buhari domin a samu sauyin gwamnati a ƙasa.

[25] Malamai ne a yau suke iya nuna mana muhimmancin sake zaɓen Buhari a matsayin shugaban ƙasa da El-Rufa’i a matsayin gwamnan Kaduna saboda irin kyawawan manufofinsu da ƙoƙarinsu wurin daidaita al’amura a jiha da ƙasa baki-ɗaya.

[26] Malamai ne suke iya bayyana mana cewa: Kashe-kashe da sace-sacen mutane da yaƙe-yaƙen babu gaira babu dalili da ake yi a yau a wasu sassa na Arewa ana yin su ne tare da haɗin baki da kuma goyon bayan wasu azzaluman daga ƙasashen Turawa domin wai a nuna wa jama’a cewa Buhari bai yi komai ba!

[27] A ƙarshe kuma malamai su ne suke da cikakken sanin cewa: A yau kam babu wani ɗan takara da ke da irin ɗabi’u da halaye da kyakkyawan tarihin da har zai iya yin takara da Buhari a wurin zaɓe kuma ya yi nasara a kansa. Sai dai ko in za a yi murɗiyar da aka saba! Don haka, bai kamata mutum ya saka ƙuri’arsa a inda ya san ba za ta yi amfani ba.

Da waɗannan dalilan ne nake ganin bai dace a hana manyan malamai kuma cikakkun masana su riƙa fayyace mana wanda ya kamata mu saka wa ƙuri’armu a lokacin zaɓe mai sarƙaƙiya irin wannan ba. Wanda ya ke cike da ƙulle-ƙulle da makirci, wanda kuma ba kowane ɗaya daga cikinmu ne ke iya gano kutungwila da maƙarƙashiyar da aka cukwikkwiya aka cusa kuma aka ɓoye a cikinsa ba.

Allaah ya ƙara mana basira da fahimta.

Allaah ya nuna mana gaskiya, mu gane gaskiya ce, ya ba mu ikon bin ta; kuma ya nuna mana ƙarya, mu gane ƙarya ce, kuma ya ba mu ikon guje mata.

Ɗan’uwanku:

Muhammad Abdullaah Assalafiy,
Markazu Ahlil-Hadeeth,
Kaduna.
23/01/2019 ɓɗƙ
(2:15 am)

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Full name of Nigerian ministers and their positions

FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...