SOYAYYA
ita ce tushen rayuwa mai inganci da ke
kawo zaman lafiya a cikin rayuwar mu ta yau da
kullum, ka so mai son ka.
MECE CE SOYAYYA?
Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa
a kanta, masana da yawa sun tattauna domin
ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a
kuma fahimce ta. Kamar haka:
Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga 6angarori biyu
na masu ‘kaunar juna (C.N.H.N.).
Muhammad Hashimu ya bayyana cewa: ‘Soyayya
ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa
bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule
su cure, su game cikin zuciya d’aya. Haka kuma
soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya
ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da
ake nufi a nan shi ne, idan mutum ya so wani
tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe
cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai
shi, ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato
kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’
Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai
sanya mu ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar
soyayya ba. Domin ita soyayya ba za a iya
siffanta yadda take ba. Sai mutum ya shige ta,
sannan zai san ta.
KASHE-KASHEN SOYAYYA.
Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:
1 Soyayya Don Sha’awa.
2 Soyayya Don Abin Duniya.
3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.
1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace
kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai
d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan
har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji
yana son wannan mutum saboda wannan abu. To
irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar
d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara
neman hanyar rabuwa da juna.
2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA
: Irin wannan
soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan
kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma
irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar
abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a
fara shirye-shiryen nesanta da juna.
3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA:
Irin
wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da
hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da
ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya,
ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta
gaskiya ce. Kuma ita ce irin soyayyar da take
d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.
MENENE SO DA KAUNA.
So da kauna, wani shauki/hali ne wanda ke kama
da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a
aikace .
Ka santuwar cewa ba kowa ke sanin abunda yake
aikatawa ba a tsakanin mu, ko kuma, me
masoyina masoyiyata ke yi man daga cikin
wannan halaye. Kowannen anayinsu ne ba tare da
mutum yasan me yake aikatawa ba, kasancewar
baya iya tantancewa tsakanin biyun nan me suke
nufi. Ko wannen su aikatasu halal ne a addinin
muslumci, saidai wani yafi wani, daraja a idan
shari'a kasancewar muhimmancin sa da
amfaninsa tsakanin masoya. Hmm nasan wasu
zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da
soyayya, tirqashi... To ka sani Madarar da zumur
ilimin soyayya tatacce daga addinin muslunci,
yake. Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya
a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take
tatatta, kuma amintatta. Wacce babu yaurada ko
ha'incin juna tsakanin masoya.
Menene Kauna?
= Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci,
domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna
ba’a amutu akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai
an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare
dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali,
ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba
haka takeba, ko anyi nasarar samun abin kaunar
ko ba’ayiba, ana cigaba da masa fatan alheri
kamar yadda kake masa a baya. Kuma ita kauna
bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani
bai kwaranyar da ita.
Galibi abinda ke kawo kauna dabi’une, wato
halaiyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga
kaunarshi.
1. SO ne sinadarin dake sanyaya zuciya kamar
yadda freezer ke sanyaya zazzafan ruwa zuwa
kankara.
2. SO ne tsuntsun dake kaikawo tsakanin zukata
mabanbanta daga karshe har sai ya sami zuciyar
da zai gina shekarsa.
3. SO ne dausayin farin ciki mai haddasa ruruwar
farin ciki mara misali.
4. SO ne siffar samin ingantacciyar rayuwa mai
alfanu.
5. SO ne tsaunin rahama mai sanya masoya
magagi gami da shantakewa a bisa tagwayen
manufofi.
6. SO ne fitilar dake haskaka zuci yayinda ta fada
cikin duhu matsananci.
7. SO ne tekun dake gudana tsakanin zukata
mabanbanta.
8. SO ne asalin rayuwa, sannan kuma abin dake
sarrafa ragamar dokin rayuwa a bisa hanya
managarciya.
9. SO ne mafarar kauna, sai so ya sami
kyakkyawan mazauni a zuci kafin kauna ta biyo
bayansa.
10. SO ne bishiyar dake tsirowa a dausayin zuci,
mai fitar da furanni kyawawa masu kyawun gani.
11. SO ne sadaukin zuci, mai ingiza zuciya filin
dagar kauna, har sai ya kafa tutarsa a bainar
zuciya.
12. SO ne ginshiki, sannan kuma tubalin kauna
sai an kafa tubalin so a zuci kafin ginin kauna ya
tabbata a matabbatar ruhi.
13. SO ne tekun dake gangarowa daga ruhi zuwa
sassa daban-daban na jiki, wanda ke fesar da
shauki a nahiyar kalbi.
14. SO ne maganin dake warkar da zuciyar data
shiga garari.
15. SO ne guguwar dake daukar, masoya, idan
guguwar so ta dauki masoya takan makantar da
idanuwansu har su rasa ganin laifin juna.
*Banbanci tsakanin SO da KAUNA
Shi so sau da dama idan masoyi bai samu
nasarar samun abin san nashiba, sai ka ga
wannan soyayyar ta koma kiyayya, wasuma har
kaga sunawa abin san nasu fatan shiga uku, Allah
ya rabamu da irin wannan SO
Ita kauna bata canzawa
* Abubuwan da ke janyosu (SO+KAUNA)
Duk abu dayane sai dai daga lokacin da aka ji
zuciya tana raya cewa, in ba’a samu wanda a ke
so ba, gara a mutu kowa ya rasa, hakan seya
nuna mana ciwa So ake yi ba Kaunaban. A
takaice dai SO tsakani da Allah shi ake kira
Kauna.
Abubuwan dake janyo SO + Kauna
– Kyau
– Kudi
– Nasaba (Dangi)
– Addini
– Ilimi
– Gaskiya
– Amana
– Kunya
– Kyauta. DS
Kalaman Baki (SO)
* Da Idanuna basu gankiba> da bazan sankiba
* Da banga murmushi a kyakykyawar fuskarkiba>
da ba zan So ki ba
* Da kunnuwana basu ji sautinkiba> da bazan jiki
a zuciyataba
* Lafazinki dadi zuciya ta yake tausasa mini
* Kayan jikinki kamshi turaranki zo ki fesa mini
* Duniyata dake nake alfahari, Sarauniyar mata
nasamu mai kwantarmin da zuciyata, Na baki
kaina kirike……
YADDA ZA KA BAYYANAR DA SOYAYYARKA.
“Wata yarinya na gani na kuma kamu da sonta,
kuma ina zuwa gidansu, yaya zan yi na bayyana
mata ina son ta?”
AMSA.
Zata iya kasancewa babba ce ko ‘karama, to
koma dai yaya take a karon farko akwai bu’katar
kafin ka furta mata da baki, kake nuna mata
wasu alamomi da zasu ke bayyana mata hakan a
zahiri. ta hanyar fifita ta fiye da sauran ‘yan
gidansu.
Idan ka tashi zuwa gidan da wata tsaraba ko
wata kyauta ya kasance tata ta fi ta kowa yawa.
Idan salla ta zo ka d’inka mata kayan salla da
takalmi da sauran kayan kwalliya na mata dai-dai
‘karfinka ka aika ko ka kai mata su. A lokacin
azumi kake aika mata da kayan shan ruwa.
Idan ka je gidansu ko da bata nan kake tambayar
ina ta tafi, idan kuka had’u ka sanar da ita ka je
gidansu dan ka gan ta ku gaisa amma sai aka
samu akasi baku had’u ba, kuma baka ji dad’in
rashin ganin nata ba.
Kake yawan jan ta da hira, kake bata labarai
masu sanya nishad’i da d’ebe kewa a dukkan
lokacin da kuke tare.
Na tabbata ko baka furta kalmar so a gare ta ba
za ta sha’ku da kai, za ka ke burge ta, za ta ke
son ganin zuwanka, haka kuma ‘yan gidansu za
su fahimci ‘kudurinka na kana sonta.
Bayan an shafe tsawan wani d’an lokaci hakan na
faruwa, sai ka ware watarana ka ziyarce ta har
gida ka aika a kirawo ta ka sanar da ita batun da
tuntuni take tsammanin ji daga wajenka, wato na
kana son ta.
Zaka iya sanar da ita ta hanyar tura mata da
sa’ko ko akasin haka, amma zuwa da kai, ya fi
sa’ko.
Idan kuma yarinya ce zaka sanar da ita hakan ne
bayan ta kai munzalin tsayawa da samari. Dama
tintini ‘yan gidansu sun dad’e da sanin manufarka
a kanta, har ta kai suna zolayarta da kai,
wata’kila ma suna yi maka magana akan hakan
ko kuma sun zuba ido suna jiran ka furta hakan
da kanka.
Daga nan kuma sai a shiga mataki na biyu wato
fagen soyayya.
YAUDARA A SOYAYYA.
Abun dai ruwan dare ne, ba ga mazan ko matan
ba.
Kowane 6angare na maza da mata suna ta6a
waccan halayya ta yaudara a soyayya kuma suna
fuskantar hakan daga abokan zamansu.
To amma shin wai mene ne yake kawo yaudara a
soyayya? Mece ce ma ma’anar kalmar yaudara?
Yaudara ita ce, hali na 6oye gaskiya da niyyar
cuta ko zambatar wani.
A lokuta da yawa maza su ke sakin jiki har mata
su yaudare su, ko kuma su mata suke
sakankancewa har maza su yaudare su a
soyayya. Ina ganin za ku yarda da ni idan na ce.
A dukkan lokacin da ka ji yaudara to da akwai
rashin so da tausayi.
MAZA:
A sau da yawan lokuta namiji kan makance a kan
soyayya har idanuwansa su rufe a kan haka, ya
gaza gane macen da ta ke son shi dan abun
hannunsa, ko ta ke kula shi kawai saboda rage
dare, ko dan wani abu da ta ke nema a wajensa,
ko macen da ta ke kula shi ba dan tana son shi
ba, sai dan kawai ya matsanta mata akan ta so
shi, da macen da ta ke son shi kawai dan tana jin
dad’in kalamansa ko jin dad’in hira da shi amma
ba dan tana son shi ba, har ta kai daga baya da
zarar ta samu wani da take so ko ta gama
cimma burinta a gare shi sai ta guje shi. Sai ka ji
daga bisani ana mayar da yawu kan cewa ai
wance ta yaudare ni, bayan kuma da ma can
babu son gaskiya a tsakani.
Domin gujewa fad’awa irin wannan halin, tun da
fari akwai bu’katar ka san wasu alamomi da
ganinsu zai tabbatar maka da cewa tabbas
wance tana sonka da gaskiya. Amma duk da haka
sai ka yi taka-tsantsan.
MATA:
Ke ma akwai bu’katar dukkan wanda ya zo miki
da batun soyayya, ki tsaya ki nutsu ki tantance
masoyinki na gaskiya, domin gujewa fad’awa
tarkon samarin shaho (‘yan-yaudara)
Akwai wani zai zo ne yana son ki kawai dan ya yi
alfahari da cewa ke budurwarsa ce. Wani kuma
zai yi ‘ko’karin neman hanyar da zai bi ya
yaudare ki ne dan ya lalata miki rayuwa. Wani
zai zo wajenki dan ya rage dare ne kawai. D.s.
Da yawan ‘yan yaudara, za su iya kashe miki ko
nawa ne, har ma su yi wa waninki hidima, dan
bu’katarsu ta biya a kanki. Sun iya kalamai masu
dad’i amma na yaudara.
Maza ‘yan yaudara suna da wahalar ganewa a
wajen mata, wani zai iya zubar miki da hawaye,
wai dan duk ki yarda ya na son ki da gaskiya, zai
iya siyo miki duk abun da kike so, zai iya baki
duk abun da kika bu’kata daga wajensa
matu’katar bu’katarsa za ta biya a kanki.
Domin gujewa hakan ya kamata kike lura da irin
kalaman da yawanci ke futa daga bakinsu, kike
tace na gaskiya da kuma na ‘karya. Karda SO ya
rufe miki ido ki gaza tabbatarwa da zuciyarki
wane yaudararki kawai yake son yi, bayan kin
gano hakan ko alamun hakan sun bayyana
‘karara a zahiri, saboda gudun yin da-na-sani
daga baya. Wanka da gari dai ba ya maganin
yunwa.
Ma’anar Aure
Abinda aka sani da aure a dukkan al’adu, yaruka
da addinai shine namiji ya samu macen da yake,
ya jawo hankalinta akan ta yarda suyi zaman
tare, ya biya haqqoqinta sannan mutane su
shaida akan cewa ta zama matarsa saboda haka
an halatta masa yin duk wasu abubuwa da kan
iya gudana tsakanin mace da namiji. Yana daga
cikin al’adun kuma cewa daga ranar ita macen
zata bar gidansu ta koma gidan shi wanda ta
zaba kuma ta aura a matsayin mijin nata.
Akan daura aure tare sharudda da yawa
wandanda suka banbanta daga al’ada zuwa
al’ada. A al’ada da addini na bahaushe,
sharuddan da sukan biyo aure sun hada da
samarda muhalli ko gurin zama ga matar, ciyar
da ita, sama mata tufafi da kuma kula da
lafiyarta.
Dalilin Yin Aure
Akwai dalilai da yawa da suka sa dole duk wani
mutum mai hankali yayi aure idan yakai munzalin
yin auren. Annabin tsira (S.A.W) yace da
al’ummarsa kuyi aure ku hayayyafa dan inyi
alfahari da yawanku ranar qiyama. Sannan Allah
SWT ya halicci mutane (maza da mata) da
sha’awa, wacce hanya daya da duk addinai suka
yarda da ayi amfani da ita wajen biyan buqatar
sha’awa shine aure. Wadannan dalilai guda biyu
ma kawai sun isa hujja ga masu cewa su basa
soyayya; sai da soyayya ne za’a iya yin aure.
Idan aka duba bangaren ibada kuma, Annabi
(S.A.W) yace wanda yai aure ya bayar da rabin
ibadarsa, sannan duk wani abu da masu aure
zasu yiwa junansu na daga jin dadi lada zasu
samu, hmn wannan itace garabasa, hanya mai
sauqi ta samun aljanna.
Yana da amfani mutum yasan wadannan
manufofi na yin aure kafin yayi aure, sannan
kuma ya dinga tuna su koda yaushe, musamman
a lokacin da aka samu sabani, hakan zai taimaka
wajen shawo kan da yawa daga cikin matsalolin
aure. Haka shima wanda yaje yin sulhu ga
ma’auratan da suka sami sabani, yana da kyau
ya tunantar dasu akan wadannan manufofi na yin
aure; Allah yasa mu dace.
WACCECE MACE TA-GARI??
1. Mace tagari ita ce wacce Idan Mijinta ya
kalleta Zai ji farinciki ya lullubeshi.
2. Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin
Mijinta.
3. Ita ce wacce take mutukar kiyaye duk abinda
zai 'bata ma Mijinta rai.
4. Ita ce wacce take dagewa wajen bautar
Ubangijinta.
5. Ita ce wacce batta wasa da duk wani Hakki na
mijinta.
6. Ita ce wacce duk lokacin da Mijinta yayi fushi,
batta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar
dashi.
7. Ita ce wacce take Kiyaye Duk wani sirrin
Mijinta.
8. Ita ce wacce idan Mijinta ba yanan take Kiyaye
mutuncin Kanta, da kuma dukiyar da ya bari
agida.
9. Ita ce Wacce take kulawa da Tarbiyyan Mijinta
da 'ya'yansa koda ba ita ce ta haifesu ba..
10. Ita ce wacce take mutukar girmama Iyayen
Mijinta kamar yadda take girmama nata iyayen..
Kuma take kyautatawa 'yan uwansa ba tare da
tsangwama ba.
11. Ita ce wacce take zama da Makobtanta da
kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa.
Koda su suna munana mata..
MIJI NAGARI ... KO KUNSAN WAYE MIJI NAGARI
Most of the time a wajen wa'azozi ko lectures ba
a cika fadawa mutane halayen miji nagariba abin
yana yawan bani mamaki akan meyasa baacewa
ga halayen miji nagari, sai dai ayita cewa halayen
mace tagari.... Ga wassu daga cikin halayen miji
nagari Shine wanda yake ciyar da iyalinsa halaliya
idan shima yaci... Yake shayar dasu idan shima
yasha.... Kuma yake tufatar dasu idan ya suturta
kansa bawai sai shekara shekaraba domin yasan
darajar kwalliyar.... Shine wanda zai zamo zaki a
waje, damo acikin gida wato me hàkuri ga dukkan
lumura... Ko kuma yazamto kamar air condition
wato a waje yake kara amman aciki sanyi yake
bayarwa.... Shine wanda ya hada wassu siffofi
guda 10 wadanda Allah Ta'ala Ya ambacesu
acikin suratul Ahzab aya ta 35. Miji nagari shine
wanda yakeson matarsa bayan aurensu fiyeda
yadda yasota a layi ya nuna mata kauna ya jata
ajiki ya sanar da ita abinda yafi faranta masa rai
ya bata Abinci a baki ya tarairayeta kamar jaririya
cikin so da kauna... Shine mai kishin matarsa.
Domin Sayyidil waraa Sallallahu alaihi wasallam
yace: "duk wanda baya kishin matarsa bazai
shiga aljannah ba". Shine wanda ya dauki aure
amatsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma
abin jin dadin rayuwa kawai ba.... Shine wanda
ya dauki matarsa amatsayin abokiyarsa,
kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar
shawararsa. Shine wanda ba ya zagin matarsa,
baya cin mutuncinta, ba ya cin zalinta, baya
ha'intarta koda a bayan idontane...... Shine
wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da
gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Shine
wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake
hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin
neman rahamar Allah Ta'ala. Shine wanda idan
zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu
yaudara ko karya acikin ayyukansa da zancensa.
Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewar: Iyayen
matarsa, Iyayensa ne. 'Yan uwanta ma 'yan
uwansa ne. Danginta ma danginsa ne. Shine
wanda yake daukar cewa farincikin matarsa shine
farincikinsa. Kuma Problem dinta, shima nasa
ne... Shine yake kokarin kiyaye sirrin matarsa,
kuma yake kokarin Kare mata mutuncinta koda
awajen 'yan uwansa ne, tare da hikima
da.fahimtarwa. Shine wanda baya fifita matarsa
akan 'yan uwansa, kuma baya tauye mata
darajarta. Yana ba ma kowanne gefe nasa
hakkinsa kamar yadda shariah ta tanadar Shine
wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri acikin
zuciyarsa domin ya rika kashe wutar tashin
hankali da bacin rai aduk lokacin da hakan ta faru
tsakaninsa da matarsa. Shine wanda a kullum
yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan
rayuwar addinin Islama ba rayuwa irinta yahudu
da nasaraba Shine wanda yake zaune da matarsa
komai da'di komai wuya ba zai dena nuna mata
soyayya ba wai don tafara yankwanewa ko kuma
karfinta yafara raguwa. Shine wanda yake bawa
matarsa compliments a duk lokacin datayi
kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi.
Miji nagari baya raki,baya ihu don yaji abinci yayi
yaji ko gishiri yayi waya. Sai dai yace: "uwargida
abincinnan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi
mana shisshigi aciki".... Shine Wanda yakeda
tausayi a duk lokacin damatarsa bata da lfy to
shima bashida lfyr yana tausaya mata matuka
yakan dauketa da kanshi ya kaita asibiti domin
tausaya mata... Kunji kadan daga cikin halayen
maza nagari.... Allah Yasa mazaje su gane, su
sauke hakkinsu na kulawa da iyali, su daina
ha'intar matansu, su daina yin dare a layi, ko
kuma cin abinci a rumfar me shayi... Ya Allah ka
bamu maza nagari... Su kuma ka basu mata
nagari ameen...
Yadda zaki mallake zuciyar mijinki!
1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina,
shagwaba dss, don namiji baya son mai halin
maza ta zama matarsa.
2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai
zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita
ko zuwa ko ina ba.
3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko
na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta
tukuna ya samu nutsuwa.
4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga
Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya
zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan
abinda kika ga alamar yana nema ya karaya,
hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza.
6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau
dayawa, dayawa dayawa, Aisha ﺭﺿﺎﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tace
Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta
qarfin soyayyarta gareshi, sai tace mishi kamar
‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance
ba), sai ya sake tambayarta ‘yaya zargen yake’?
Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka
miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi
dake fiye da yadda kike farin ciki dani!
7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen
gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya dss).
8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a gida;
kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai
sa ya qara dagewa.
9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin
alheri
10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci,
da yardar Allah sai kiga ya dawo dai dai.
11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki
abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma!
12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da
farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi
wajen yanke hukunci.
13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan
qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi
haquri kuma ki dena.
14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo sabod
Allah, sai kiga Allah ya sa miki albarka a cikin
duk abinda kike yi.
Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi da
ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure!
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Featured Post
Full name of Nigerian ministers and their positions
FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...

-
UDUSOK Admission List 2018/2019 Academic Session Out mcmedal001 October 1, 2018 Admission Lists Usmanu Danfodiyo University, Sokoto,...
-
FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...
-
DENTAL HEALTH EDUCATION ORAL AND GENERAL HYGIENE The above mentioned topic has been opted to be discuss in this forum in co...
No comments:
Post a Comment