Thursday, February 21, 2019

Hanyoyi 21 na samun rayuwa me albarka

HANYOYI GUDA 21 NA SAMUN RAYUWA MAI ALBARKA

 *Darasi na Biyu-(2)*

*5-SADAKA*
Bada saka da kyauta yana cikin mafi girma hanyar samu rayuwa mai albarka,domin sadaka maganice ta tun kude masifa da bala'i ga mai yinta daga iyalinsa da dukiyarsa,kuma Sadaka hanyace ta waraka daga dukkan wasu cutuka da samun walwala da sanyi zuciya da samun karbuwa da soyayya ga yan'uwa da dangi da sauran al'umma,sannan Sadaka alamace ta tabbatuwar Imani ga mai yinta,sannan Sadaka tana sanyawa dukiyar mai yinta albarka da kariya daga lalacewar dukiya,Mala'ika yana yiwa mai Sadaka adduar Allah ya sanya albarka a dukiyarsa da kuma kareta daga dukkan matsala,akowane yini Mala'ika yana yin wannan adduar ga mai yin Sadaka,Sadaka tana sanyawa arubunya dukiyarka ta kuma habaka".

Allah yana cewa:-
(ﻗُﻞْ ﺇِﻥَّ ﺭَﺑِّﻲ ﻳَﺒْﺴُﻂُ ﺍﻟﺮِّﺯْﻕَ ﻟِﻤَﻦ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﻣِﻦْ ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ ﻭَﻳَﻘْﺪِﺭُ ﻟَﻪُ ۚ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﻧﻔَﻘْﺘُﻢ ﻣِّﻦ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﻬُﻮَ ﻳُﺨْﻠِﻔُﻪُ ۖ ﻭَﻫُﻮَ ﺧَﻴْﺮُ ﺍﻟﺮَّﺍﺯِﻗِﻴﻦَ)

*(Ka ce:"Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa,kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to,Shĩ ne zai musanya shi,kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa)*.
!ﺳﺒﺄ ‏( 39 ) Saba

(ﻳَﻤْﺤَﻖُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﺮِّﺑَﺎ ﻭَﻳُﺮْﺑِﻲ ﺍﻟﺼَّﺪَﻗَﺎﺕِ ۗ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳُﺤِﺐُّ ﻛُﻞَّ ﻛَﻔَّﺎﺭٍ ﺃَﺛِﻴﻢٍ)

*(Allah Yana shãfe albarkar riba,kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci,mai zunubi)*
@ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ ‏( 276 ) Al-Baqara

Annaabi s.a w yana cewa:-
*(Dukiyar bawa bata taba raguwaba saboda Sadaka,babu abinda bawa zai samu idan yayi afwa face Izza,Kuma babu wani bawa da zai kankantar da kansa ga Allah,face Allah ya daukaka shi)*.
@ﻣﺴﻠﻢ 2588
 ‏) ،ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 2029 ) .

*(Babu wanda zaiyi sadaka da kwatankwacin Dabino daga dukiya ta halas mai tsarki, domin Allah Ta'ala mai tsarkine baya amsar aiki sai mai tsarki,face sai Allah ya karbi wannan sadaka yana kuwa da ita kamar yadda dayanku yake kulawa da shularsa har sai wannan sadaka ta koma kamar girman Uhudu)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 7430 ‏) ، ﻭﺃﺣﻤﺪ ﻓﻲ \" ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ \"( 7622 ‏) ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
‏( 661 ‏) ،ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2525 ‏) ،ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ

*(Annaabi ya bada kisssa mai tsawo ta mutum da yaji aciki gajimarai ana cewa a shayar da gonan wane,Saboda mutuman ya kasance yana sadaka da daya bisa ukku na abinda ya noma sai Allah ya sanya akayi ruwa aka shayar da gonansa shi kadai saboda da girman sadaka)*.
@ﻣﺴﻠﻢ ‏( 2984 ‏) ،ﻭﺃﺣﻤﺪ ‏( 7928 )

*6-KUSANTAR ALLAH TA HANYAR AIKIN NAFILA BAYAN SAUKE FARILLAI*

nnaabi s.a.w yana cewa;-
*(........Kuma bawana bai taba samun kusanci dani ba da wani abu ba fiye da abinda na wajabta masa,Kuma bawana bazai nemi kusanci dani ba tahanyar Aikata nafilfili har sai naso shi,idan Nasosa sai na kansance jinsa wanda yake ji da shi, ganinsa wanda yake gani da shi,hannunsa wanda yake damqa dashi,kafarsa wanda yake tafiya da ita,Idan yaroke zan amsa masa kuma na bashi abinda yake roko kuma da zai nemi kariyata zan bashi.....)*.
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 6502 ‏)

*7-GODEWA ALLAH AKAN DUKKAN NI'IMAR DA YAYI MAKA*

"Godiya ga ni'imar Allah ga bawa ta hanya guda ukku:-

*A-Yarda a zuciya wannan ni'imar daga Allah take shi kadai*.

*B-Bayyanawa da nunawa al'umma Allah yayi maka ni'ima batare da alfahari ba*.

*C-Yin amfani da wannan ni'imar ta hanyar yin biyayya da dha'a ga Allah*.

Wanda Allah yayi masa wata ni'ima sai yayi abubuwa guda ukku hakika yayi Shuka da godiya ga Allah,sai Allah ya sanyawa wannan abu da ya bashi albarka kuma ya kara masa wata ni'imar.

Godiya ga ni'imar Allah yana sanyawa Allah ya sanya albarka a rayuwar bawa kuma ya kara masa wata ni'imar wadda tafi wadda ya basa.

Allah yana cewa:-
ﻭَﺇِﺫْ ﺗَﺄَﺫَّﻥَ ﺭَﺑُّﻜُﻢْ ﻟَﺌِﻦ ﺷَﻜَﺮْﺗُﻢْ ﻟَﺄَﺯِﻳﺪَﻧَّﻜُﻢْ ۖ ﻭَﻟَﺌِﻦ ﻛَﻔَﺮْﺗُﻢْ ﺇِﻥَّ ﻋَﺬَﺍﺑِﻲ ﻟَﺸَﺪِﻳﺪٌ)

*(Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, "Lalle ne idan kun gõde,haƙĩƙa,Inã ƙãramuku,kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta,tabbas, mai tsanani ce)*.
@ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ‏( 7 ) Ibrahim

Annabi s.a.w ya bada labarin:-
*(mutane guda ukku na bani israa'ila makaho da kuturu da mai kora wanda Allah ya jarabce su kuma dukkan su babu wanda ya godwe Allah akan ni'imar da yayi masa face mutum daya makaho sai Allah ya sanya albarka akan abinda ya basa yayi rayuwa mai dadi sauran kuwa da basu godewa ni'imar da Allah ya yi masu sai Allah ya amshi ni'imar sa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ‏( 3464 ‏) ،ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 2964 ‏) .

*Mu hadu a darasi na gaba insha Allah*

Allah ne mafi sani.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Full name of Nigerian ministers and their positions

FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...