Monday, February 11, 2019

LOKUTA BIYAR (5) DA AKE BUDE KOFOFIN SAMA

*_LOKUTA GUDA-(5) BIYAR DA AKE BUDE KOKOFIN SAMA_*

-Kafin Sallar Azzuhur.
Manzon Allah SAW yana cewa:
*_(Lallai ana bude kokofin sama lokacin da rana tayi zawali ba'a kullesu har sai anyi Sallar azzuhur, shi yasa nake so aiyukan alkhairi nawa ahau sama dasu a wannan lokacin)_*.
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 1532 )

NB
_"Shi yasanya Annabi s.a.w ya sunnan ta mana yin nafila raka'a hudu a awannan lokacin kamar yadda yazo a cikin"_.
@Saheeha.

2-Lokacin kowane kiran sallah.
Manzon Allah s.a.w yace:
*(Idan kayi kiran Sallah ana bude kokofin sama,kuma sai a amshi adduar wanda yayi addua a wannan lokacin)*.
@ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ‏( 260 ‏) ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 818 ).

NB
_"Dan haka mu yawaita rokon Allah bayan kiran sallah lokacine na amsa addua kamar yadda Annabi s.a.w yace"_.

3-Lokacin jiran sallah a masallaci bayan an gama wata sallah,kamar tsakanin magariba da Isha'i ko tsakanin La'asar zuwa Magariba.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Kuyi albishir,wannan Ubangijinku ne ya bude wata kofa daga cikin kokofin sama,yana alfahari da ku a wajan mala'ikunsa yana cewa:ku kulli bayina sun gabatar da farilla dana dora masu kuma amma suna jiran wata sallar)*.
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ‏( 445 ‏) ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 36 )

NB
_"Wanda ya zauna a wajan sallarsa yana jiran wata sallah mala'iku sunayi masa addua kuma ana rubuta masa ladar yana cikin sallah sannan ana bude masa kofar sama dan amsa adduarsa"_

*4-Idan dare yayi Rabi*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Idan dare yayi rabi ana bude kokofin sama,sai wani mai kira yayi kira yace: Shin akwai mai rokon Allah a amsa masa?akwai mai roko abashi?akwai mai da damuwa a yaye masa?babu wani musulmi da zai roki Allah a wannan lokaci face Allah ya amsa masa,sai dai mazinaciyar da take amfanuwa da zinar ko kudin zina....)*.
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ - ﺭﻗﻢ : ‏( 786 ‏)
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 2971 )

*5-Lokacin yin addua da wadan nan kalmomi*:

*ﺍﻟﻠﻪُ ﺃﻛﺒﺮُ ﻛﺒﻴﺮًﺍ ﻭﺍﻟﺤﻤﺪُ ﻟﻠﻪ ﻛﺜﻴﺮًﺍ ﻭﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪِ ﺑﻜﺮﺓً ﻭﺃﺻﻴﻞً*ﺍ
[ALLAHU AKBAR KABIRAN WALHAMDU LILLAHI KATHIRAN WA SUBHANALLAH BUKRATAN WA ASILA*]

Daya daga cikin sahabban Manzon s.a.w yana cewa:
"Wani lokaci muna sallah tare da Manzon Allah s.a.w sai wani mutum daga cikin mutane yace:
[ﺍﻟﻠﻪُ ﺃﻛﺒﺮُ ﻛﺒﻴﺮًﺍ ﻭﺍﻟﺤﻤﺪُ ﻟﻠﻪ ﻛﺜﻴﺮًﺍ ﻭﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪِ ﺑﻜﺮﺓً ﻭﺃﺻﻴﻞ]
*ALLAHU AKBAR KABIRAN WALHAMDU LILLAHI KATHIRAN WA SUBHANALLAH BUKRATAN WA ASILA*]
sai Manzon Allah s.a.w yace:
*(Wanene ya fadi wadan nan kalmomin??)* Sai wani mutum yace nine ya Manzon Allah. Sai yace:
(An amsa adduarka kuma an bude maka kofofin sama,saboda da wadan nan kalmami)*.

Ibn Umar R.A yake cewa:
*"Ban taba barin fadar wadan nan kalmomin ba lokacin addua tun daga lokacin da naji Manzon S.a.w ya fadi haka"*.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 601 ).

Mu hada wannan muyi turawa yan uwan mu domin amfanin juna duniya da lahira.
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻤﺒﺎﺭﻙ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:
"Ban san wata daraja mafi falala da daukaka bayan Annabta kamar yada Ilimi mai amfani".
@ﺗﻬﺬﻳﺐ ﺍﻟﻜﻤﺎﻝ ‏( ٢٠ /١٦ ).

Allah ya sanya mu cikin wadan da ake amsa adduar su.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Full name of Nigerian ministers and their positions

FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...