Saturday, May 4, 2019

Mene ne azumi

MENE NE AZUMI??

. AZUMI A LUGGA:-Shine kamewa
2. ASHARI'ANCE:- Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

RUKUNAN AZUMI

1. Yin niyya
2. Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali
3. Zamani (lokachin yin azumi).

SUNNONIN AZUMI
1. Jinkirta buda baki har sai rana ta fada
2. gaggauta sahur karba alfijir ya keto.
3. Addu'a yayin buda baki
4. Yin sahur da gaggauta shi kar alfijir ya keto.
br /> MAKARUHAN AZUMI
1. Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
2. Sumba
3. Dauwamar da kallo na sha' awa
4. Tunani akan al'amuran saduwa
5. Shafa ko runguma
6. Dandanan wani abu
7. Sanya tozali
8. Yin kaho.

ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI
1. Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
2. Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
3. Saduwa ta hanyar tilasta
4. Chi ko sha da tunanin sauran dare
5. Chi ko sha da mantuwa
6. Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi
7. Ridda.

ABUBUWAN DA SUKE HALAS
1. Yin asiwaki
2. Sanyaya jiki da ruwa
3. Tafiya ta halas
4. Sanya magani wanda ya dache
5. Tauna wani abu ga karamin yaro
6. Sanya turare.

BUBUWAN DA AKAYI RANGWAME
1. Hadiye yawu
2. Rinjayen amai da magwas
3. Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
4. Kuran kan hanya
5. Wayan gari da janaba
6. Yin mafarki da rana.

Allah yabamu ikon aiki da shi. Ameen Thummah Ameen

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Full name of Nigerian ministers and their positions

FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...