Friday, April 12, 2019

Fiqiwu a saukake

.                *FARILLAN ALWALA*


arillan alwala guda 7 neh:
• Niyya
• Wanke Fuska
• Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
• Shafar kai
• Wanke kafafuwa
• Cuccudawa
• Gaggautawa

                  *SUNNONIN ALWALA*

• Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
• Kurkure baki
• Shaka ruwa
• Fyacewa
• Juyo da shafar kai
• Shafar kunnuwa
• Sabunta ruwa agaresu
• Jeranta tsakanin farillah

             *MUSTAHABBAN ALWALA*

• Yin bismillah
• Goga asuwaki
• Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye

Farawa daga goshi
• Jeranta sunnoni
• Qaranta ruwa a nisa gabobi
• Gabatar da dama kafin hau.

              *AKAN FASALIN ALWALA*

• Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun.

• Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba.

• Wanda kuma ya mance lam'a sai ya wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah by an faruwar hakan toh sai ya sake ta

• Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to bazai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai yayi su

• Tsettsefe 'yan yatsu hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe 'yan yatsun qafafuwa, tsefe gemu mara dubu yana wajaba acikin alwala, tsefe gemu yana wajaba acikin wanka koh da mai duhu neh.
br />           *AKAN FASALIN ALWALA  (2)*

• Babu yana halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur'ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan *juzu'i* neh ga mai neman ilimi acikinsa. 


Yaro a wajen taba al qur'ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya bashi al qur'anin ya taba.

• Wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah ya ki ya she mu.

*ABUBUWA MASU WARWARE ALWALA*

*_Karrai da Sababai_*

                           *Karrai sune:*
• Fitsari
• Bayan gida
• War rihu (tusa)
• Maziyyi
• Wadiyyi

                          *Sababai sune:*
• Bacci mai nauyi
• Suma
• Farfadiya
• Marisa
• Maye
• Hauka
• Sumbata
• Shafar mace, idan anyi da niyyar jindadi ko kuma ya samu jindadin babu nufi
• Shafar azzakarinsa da cikin hannu ko da cikin 'yan yatsu duk ta warware.

°Wanda yayi ko kwanto acikin samuwar kari to alwala ta wajaba agareshi, saidai in mai yawan waswasi neh, to babu komai agareshi.
°Yana wajaba agareshi ya wanke dukkanin azzakarinsa saboda fitowar maziyy.
°Shi maziyy wani ruwa ne da yake fitowa lokacin 'yar sha'awa karama, ta yin tunani koh kallo koh yin wanin wannan.


nbsp;             *BAYANIN TSARKI*

_tsarki kashi 2 neh:_
°Tsarkin kari
°Tsarkin dau'da

• Dukkan su basa inganta saida ruwa mai tsarki, mai tsarkakewa shine: wanda kamarsa bata jirkita ba, ko dandanon sa, ko qamshinsa, da abunda yake rarrabe shi marinjayi. Babu laifi da kasar gishiri da kasar kanwa da makamancinsa.

• Idan najasa ta fito fili sai a wanke gurin, idanta fantsama sai a wanke tufar gabadaya. Wanda yayi kokwanto acikin samuwar najasa, to sai yayi yayyafi da ruwa ajikin kayan.

• Idan kuma wani abu ya sameshi sai yayi kokwanto acikin najastuwarsa, to ba sai yayi yayyafi ba.

• Wanda kuma ya tuna da najasa yana cikin sallah sai ya yanke sallar, saidai idan yaji tsoron fitar lokaci. Wanda yayi sallah da ita yana mai mantuwa sai ya tuna bayan yayi sallama to ya sake sallah idan da lokaci.

Allah ya karbi Ibadunmu yasa mu cika da Imani.


a kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daya daga cikin Abubuwan da suke kusanta bawa ga Mahalicci.
___________________________

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Full name of Nigerian ministers and their positions

FULL LIST OF THE NEW MINISTERS 1) Dr. Uchechukwu Ogah – Abia, Mines and Steel Development, State 2) Muhammed Musa Bello – Adam...